Isa ga babban shafi

Kungiyar Tarayyar Turai ta gurfanar da kamfanin Tik-Tok

Kungiyar Tarayyar Turai ta gurfanar da kamfanin manhajar Tik-Tok a gaban kotu, bisa zargin sa da kin biyayya ga dokokin kasa da kasa na kare kananan yara.

Tambarin kamfanin Tik-Tok kenan
Tambarin kamfanin Tik-Tok kenan REUTERS - Dado Ruvic
Talla

Tarayyar Turai ta zargi kamfanin da yin fatali ga dokokin kula da ‘yancin kanan yara da kuma hana su amfani da manhajar har sai sun mallaki hankali su.

Ga duk masu amfani da manhajar ta Tik-Tok za su lura da yadda wasu mutanen kan yi amfani da kananan yara ta hanyar da bata dace ba, ko kuma yadda kananan yaran ke da shafuka na kashin kansu, abinda ya kasance haramun bisa dokokin duniya.

Wannan itace kara ta biyu da kungiyar ta shigar da kamfanin na Tik-Tok tun bayan da manhajar ta sami karbuwa tsakanin mutane.

Brussels dai na ganin cewa kamfanin mallakin kasar China ya ki biyayya ga dokokin, musamman na hana kananan yara mallakar shafuka don haka ya kamata a hukunta shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.