Isa ga babban shafi

EU za ta takaita amfani da fasahar sanya wa na'urori basirar dan adam

Majalisar kungiyar kasashen Turai EU ta dauki matakin farko na fadada dokokin sa ido da kuma takaita amfani da fasashohin na’ura mai kwakwalwa da suke da karfin taimaka wa dan Adam wajen gudanar da ayyukansa, kama daga fannin kere-kere, binciken ilimi da sauran lamurran yau da kulllum. 

Kasashen da suka ci gaba dai na ci gaba da fito da sabbin dabarun amfani da na'ura mai kwakwalwa.
Kasashen da suka ci gaba dai na ci gaba da fito da sabbin dabarun amfani da na'ura mai kwakwalwa. © canva
Talla

A wannan Alhamis kwamitocin majalisar kungiyar kasashen Turai da suke bibiyar lamurran 'yancin walwala da kuma kare hakkokin masu sayen kayayyaki da kuma biyan ladan yi musu ayyuka suka kada kuri'a da gagarumin rinjaye.

Kuri'ar dai ta ta'allaka ne, kan amincewa da kudirin kafa dokar takaita hanyoyin da za a iya yin amfani da fasahar da ke bai wa na’urori musamman na komfuta karfin kwaikwayon basirar dan Adam, waddda aka fi sani da AI wato Artificial Intelligence a turance , duk da cewar  suna goyon bayan a cigaba da bunkasa nazarin kimiyyar fannin. 

A wata mai zuwa ne za a gabatar da wannan kuduri ga cikakken zama na zauren majalisar dokokin kungiyar EU, daga bisani kuma gwamnatocin kasashen yammacin Turan su tattauna domin cimma matsaya ta karshe akan batun. 

'Yan majalisar na EU dai sun bayyana kuri’ar da suka kada a matsayin tarihi babba, matakin da suke fatan zai basu damar zama na farko da za su kafa dokokin farko a hukumance da suke sa ido da kuma takaita amfani da fasahar sanya na’urori basirar dan Adam. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.