Isa ga babban shafi

Kumbon 'yan sama jannati mafi girma ya tarwatse jim kadan bayan tashinsa

Kumbon ‘yan sama Jannati, mafi girma da aka taba kerawa mai suna ‘Starship’, ya tarwatse a lokacin gwajin tashinsa na farko daga jihar Texas ta Amurka a ranar Alhamis 20 ga watan Afrilu.

Jirgin 'yan sama jannati na 'Starship' da kamfanin SpaceX ya kera,  bayan harba shi zuwa sararin samaniya daga jihar Texas da ke Amurka.
Jirgin 'yan sama jannati na 'Starship' da kamfanin SpaceX ya kera, bayan harba shi zuwa sararin samaniya daga jihar Texas da ke Amurka. AP - Eric Gay
Talla

Sai dai hamshakin attajirin duniya Elon Musk ya taya tawagar kwararrun kamfaninsa na SpaceX murna kan nasarar da suka samu ta kera jirgin saman jannatin da ka iya aika mutane da tarin kaya zuwa wata, duniyar Mars da ma sauran dunuyoyin da ke da nisan gaske a sararin samaniya.

Jirgin 'yan sama jannati na 'Starship' da kamfanin SpaceX ya kera wanda aka yi gwajin harba shi, bayan rikitowarsa daga sararin samaniya, inda ya fada gabar tekun Mexico.
Jirgin 'yan sama jannati na 'Starship' da kamfanin SpaceX ya kera wanda aka yi gwajin harba shi, bayan rikitowarsa daga sararin samaniya, inda ya fada gabar tekun Mexico. AP - Eric Gay

Jirgin na Starship ya tarwatse ne, bayan da aka samu tangardar nau’rar da ta hana rabuwar jirgin ‘yan sama jannatin da kumbon, wanda aka tsara za su  rabu bayan mintuna 3 da harba su, abinda ya sa rokar tarwatsewa suka kuma fada gabar tekun Mexico.

Duk da gaza shafe tafiyar mintuna 90 da zai bai wa kumbon sama jannatin damar hawa kan falakin da duniyoyi ke kai kawo akai a sararin samaniya, mamallakin kamfanin na SpaceX Elon Musk, ya bayyana gwajin a matsayin wanda yayi nasara.

Da fari an tsara za a yi gwajin harba  kumbon na Starship ne tun a ranar Litinin, amma aka tsawaita wa’adin zuwa ranar Alhamis 20 ga watan Afrilu, saboda wasu dalilai na kokarin gyara tangardar na’ura.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.