Isa ga babban shafi

India ta dukufa wajen samar da magunguna rage kiba

Kamfanonin harhada magunguna a India sun dukufa wajen samar da nau’ikan allurai ko kuma magungunan da ake amfani da su wajen rage kiba wadanda aka fi sani da Wegovy a turance.

Matakin na zuwa ne bayan karuwar masu teba a kasar
Matakin na zuwa ne bayan karuwar masu teba a kasar REUTERS/Finbarr O'Reilly/Files
Talla

Yunkurin kwararrun na India na zuwa ne a daidai lokacin da wasu manazarta ke hasashen bunkasar kasuwar cinikayyar magungunan na rage kiba zuwa darajar kimanin dala biliyan 100 a kowace shekara, ko ma fiye da haka nan da shekaru 10 masu zuwa.

Wannan kokari na kamfanonin harhada magungunan India dai zai taka muhimmiyar rawa wajen samun wadatar magungunan rage taiba da kuma saukin farashinsu a sassan duniya.

Tuni dai fitattun kamfanonin hada magunguna da suka hada da Sun Pharma da Cipla da kuma Lupine suka fara aikin samar da nau’ikan maganin rage kibar na Wegovy, maganin da a baya kamfanin Novo Nordisk yayi fice wajen samar da shi a fadin duniya, baya ga magungunan cutar siga da yake kan gaba wajen hadawa.

Sai dai binciken baya bayan nan ya nuna cewar katafaren kamfanin na Novo Nordisk ya gaza samar da isassun magungunan rage kibar na Wegovy ga kasashe fiye da 6, wadanda kuma a yanzu haka ke fama da matsalar yawaitar masu taiba, wadanda ke neman hanyoyin magance lalurar tasu cikin sauki ba tare da jigata ta hanyar yin atasaye ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.