Isa ga babban shafi

Taron G20 ya goyi bayan samar da halastacciyar kasar Falasdinu

Taron ministocin wajen kasashen G20 a Brazil ya goyi bayan samar da kasar Falasdinu mai cin gashin kanta a wani mataki da zai kawo karshen rikicin da ke tsakanin yankin da Isra’ila tsawon shekaru.

Ministan harkokin wajen Brazil, Mauro Vieira a jawabinsa yayin taron na G20 a birnin Rio de Janeiro.
Ministan harkokin wajen Brazil, Mauro Vieira a jawabinsa yayin taron na G20 a birnin Rio de Janeiro. AFP - MAURO PIMENTEL
Talla

Taron na yini biyu da ya gudana birnin Rio de Janeiro, kacokan ya mayar da hankali kan yakin Isra’ila a Gaza da zuwa yanzu ya kashe Falasdinawan da yawansu ya ke kokarin zarta dubu 30.

Taron ya zo ne a dai dai lokacin da Isra’ila ke barazanar tura dakaru ta kasa zuwa Rafah a hare-haren da ta ke ci gaba da kai wa wanda Brazil ta bayyana da kisan kare dangi.

Ministan harkokin wajen Brazil Mauro Vieira ya bayyana cewa hanya daya tilo ta samar da cikakken 'yanci ga Falasdinawa tare da kangesu daga duk wata barazana shi ne samar musu da kasa mai cin gashin kai, kudirin da ya shafe tsawon shekaru a zauren Majalisar Dinkin Duniya ba tare da sahale shi ba.

A bangare guda babban jami’in da ke kare manufofin EU a ketare Josep Borrell ya ce matsayar da taron ya cimma ita ce mafita a rikicin bangarorin biyu wajen ganin an samar da kasar Falasdinu mai cin gashin kanta, da kuma janyewar yahudawa ‘yan kama guri zauna da ke ci gaba da mamaye yankunan Falasdinu.

Ministan wajen Turkiya Hakan Fidan ya bukaci gaggauta tsagaita wuta a Gaza tare da kange duk wani yunkurin Isra’ila na tagayyara al’ummar Rafah, birnin da ke dauke da tarin ‘yan gudun hijira.

Duk da yadda ofishin jinkai na Majalisar Dinkin Duniya ke ci gaba da kira ga Isra’ila wajen ganin ta bayar da damar shigar da abinci da magunguna ga Falasdinawa miliyan 2 da 300 wadanda hare-haren nata ya tagayyara ko a baya-bayan nan dakarun na Isra’ila sun bude wuta ga tawagar motocin agajin da ke shirin shiga Gaza.

Zuwa yanzu adadin Falasdinawa dubu 29 da 410 Isra’ila ta kashe yayinda ta jikkata wasu dubu 69 da 465 baya ga kame wasu dubbai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.