Isa ga babban shafi

Cin zarafin musulmi na kara kamari a Indiya - Rahoto

Kididdiga ta nuna cewa kyara, tsangwama da kuma kalaman cin zarafi kan musulmi na karuwa a India musamman cikin watanni 6 da suka gabata.

Mabiya addinin muslunci kenan, yayin gudanar da zanga-zangar adawa da cin zarafin da ake nuna musu a kasar Indiya.
Mabiya addinin muslunci kenan, yayin gudanar da zanga-zangar adawa da cin zarafin da ake nuna musu a kasar Indiya. AP - Bikas Das
Talla

Wata kungiya da ke sanya idanu kan yanayin rayuwar mabiya addinai a birnin Washington ta ce rikicin Isra’ila da Hamas ya kara ta’azzara cin zarafin musulman a India.

Hukumar da ke kididdige korafe-korafen cin zarafi ta India ta ce ta karbi korafi daga mabiya addinin musulunci guda 668 a bara kadai wanda ya fi tsanani a watanni 6 na karshen shekarar.

‘Yan addinin Hindi sune ke da kaso 75 cikin 100 na cin zarafi ko izgilanci da ake yiwa musulmi a India kamar yadda kungiyar ta sanar.

Kungiyar ta ce duk da wadannan korafe-korafe, babu wani abu da gwamnatin Narendra Modi ke yi na tsare mutuncin musulmin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.