Wace ce Rumy Alqahtani wadda za ta wakilci Saudiya a gasar kyau ta duniya?
Rumy Alqahtani ta kafa tarihin zama mace ta farko wadda za ta wakilci Saudiya a gasar sarauniyar kyau ta duniya da za a gudanar a wannan shekara ta 2024.
Wallafawa ranar:
A lokacin da take sanar da labarin a shafinta na Instagram, Alqahtani ta bayyana farin cikinta na kasance ta farko da ke wakiltar Saudiya a irin wannan gasa.
An karrama ni domin shiga gasar sarauniyar kyau ta duniya a 2024. Wannan ne karon farko da Saudiya ke shiga gasar. Inji Alqahtani
Abubuwa shida game da Rumy Alqahtani
1- Matashiyar 'yar asalin birnin Riyadh ta kasance fitacciyar mai tallar kayayyakin kawa da suka hada da tufafi musamman a muhimman wurare na manyan bukukuwa da tarukan ado.
2- Ta fafata a jerin gasa daban-daban na kasa da kasa da suka hada da gasar sarauniyar kyau ta Asia da aka gudanar a Malaysia da gasar sarauniyar kyau ta zaman lafiya a yankin Larabawa da kuma gasar sarauniyar kyau a Turai.
3- Matashiyar 'yar shekaru 27 ta lashe lambobin yabo da dama a matsayinta ta mai tallace-tallacen kayan ado da kawa a yankin kasashen Larabawa da ketare.
4- Ta kammala karantu na digiri a fannin kula da lafiyar baki da hakora.
5- Baya ga harshen Larabci, Alqathani kwararriya ce a harsunan turancin Ingilishi da Faransanci
6- Kyakkyawar na da kimanin mutane miliyan 1 da ke bibiyar ta a shafinta na Instagram.
Yanzu haka matashiyar za ta wakilci Saudiya a gasar sarauniyar kyau ta duniya da za a gudanar a Mexico a bana a cikin watan Satumba mai zuwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu