Taiwan ta gamu da mummunar girgizar kasa mafi muni cikin shekaru 25
Akalla mutane 9 ne suka rasa rayukansu a girgizar kasa mafi muni ta baya-bayan da aka samu cikin shekaru 25 a Taiwan, sannan akwai wasu sama da 700 da suka samu raunuka.
Wallafawa ranar:
Hukumomin kasar sun ce, jami’an bada agaji na ci gaba da aikin ceto wadanda suka makale a cikin gidaje da dama da lamarin ya shafa.
A cewar wani malamin asibiti a Taipei, Chang Yu-lin, girgizar kasar mai karfin maki 7 da 2, ta afka wa yankin gabashin kasar ne da ke da yawan jama’a.
Girgizar da ake same ta a nisan kilomita 15.5, ta faru ne a daidai lokacin da mutane ke tafiya aiki da zuwa makaranta, wacce kuma ta haifar da baraznar tasowar tsanami a kudancin Japan da kuma Philippings, duk da cewa daga baya an ce ta kau.
Wani hoton bidiyo ya nuna yadda jami’an kai dauki ke amfani da tsani, wajen kubutar da wadanda suka makale a gine-ginen benaye ta taga.
Jami’an kashe gobara sun ce har yanzu akwai kusan mutane 60 daga cikin kusan 77 da suka makale a hanyoyin karkashin kasa da ke arewacin birnin Hualien, cikinsu kuwa harda Jamusawa biyu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu