Isa ga babban shafi

EU ta lafta sabbin takunkumai kan Iran saboda harin da ta kai Isra'ila

Shugabannin kasashen EU sun cimma jituwar amincewa da lafta sabbin takunkumai kan Iran game da harin da ta kai Isra’ila a karshen mako.

Shugabannin kasashen EU yayin taronsu na birnin Brussels.
Shugabannin kasashen EU yayin taronsu na birnin Brussels. © Yves Herman/Reuters
Talla

A daren jiya Laraba ne shugaban hukumar gudanarwar Turai Charles Michel ya sanar da matakin sabbin takunkuman na Tehran wadanda za su shafi kamfanoni da daidaikun mutane.

Matakin na EU na zuwa a dai dai lokacin da ministocin wajen kasashen G7 ke wani taro a tsibirin Capri na Italiya taron da shi ma ya mayar da hankali kacokan ga rikicin yankin gabas ta tsakiya musamman hare-haren na Iran kan Isra’ila a makon jiya.

Taron wanda aka faro jiya Laraba za kuma a kwashe kwanaki 2 ana yi gabanin karkarewa a ranar juma’ar makon nan, akwai yiwuwar ya kai ga matsayar lafta sabbin takunkumai kan Iran dai dai lokacin da ake fargabar yiwuwar Isra’ila ta mayar da martani kan Tehran.

Gamayyar kasashen na EU da na G7 sun ce sam hare-haren na Iran ba abin lamunta ba ne, wanda ke nuna dole a dakatar da kasar wadda tun tuni ke fuskantar tarin takunkuman karya tattalin arziki daga kasashe saboda shirinta na mallakar nukiliya.

Sai dai masana na ci gaba da gargadi kan abin da ka je ya zo, matukar Isra'ilan ta yi yunkuri mayar da martani kan Iran, wanda ka iya zama rincabewar rikicin gabas ta tsakiya.

Tun farko Isra'ila ta fara kai farmaki kan ofishin jakadancin Iran da ke birnin Damascus a Syria tare da kisan tarin dakarun juyin-juya halin Tehran da ke ofishin lamarin da Iran ta sha alwashin daukar fansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.