Isa ga babban shafi

Manyan kasashen Larabawa sun kauracewa taron ministocinsu a Libya

Manyan kasashen Larabawa sun kauracewa taron ministocinsu da gwamnatin rikon kwarya ta Libya ta shirya karbar bakunci a ranar Lahadi.

Najla al-Mangoush, ministar harkokin wajen gwamnatin kasar Libya mai hedikwata a birnin Tripoli.
Najla al-Mangoush, ministar harkokin wajen gwamnatin kasar Libya mai hedikwata a birnin Tripoli. AFP - RYAD KRAMDI
Talla

Bayanai sun ce biyar daga cikin kasashe 22 na kungiyar kasashen Larabawa ne kawai suka aike da manyan jami’ansu na diflomasiyya, yayin da sauran suka kaurace, ciki kuwa har da sakatare janar na kungiyar Larabawan.

Lamarin dai ya bayyana yadda aka samu rarrabuwar kawuna a tsakanin kasashen Larabawa kan gwamnatin Tripoli, wadda abokiyar hammayarta da ke gabashin kasar karkashin Kwamanda Khalifa Haftar ke adawa da halaccinta.

Manyan kasashen yankin Larabawa da suka hada da Masar, da Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa ba su tura wakilcin kowa ba zuwa wurin taron, wanda ke zama na share fagen taron da ministocin harkokin wajen kasashen Larabawan da za su yi a birnin Alkahira.

Tuni dai Najla al-Mangoush, ministar harkokin wajen gwamnatin Tripoli ta yi Allah wadai da abin da ta kira kokarin da wasu bangarorin ke yi na wargaza muradin 'yan kasar Libya dangane aniyar su ta tabbatar da hadin kan Larabawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.