Isa ga babban shafi

Lokaci ya yi da Syria za ta koma cikin rukunin kasashen Larabawa - Mohammed ben Zayed

Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya shaidawa takwaransa na Syria a Bashar Al Assad cewa, lokaci ya yi da Syria, wacce ta dade a kebe a fannin diflomasiyya, za ta koma cikin jerryn kungiyoyin Larabawa, shugaban na fadar haka yayin wani taro a Abu Dhabi.

Shugaban Syria Bashar Al-Assad, yayin wata ziyara kasar Turkiya a ranar 8 ga watan Mayun 2010
Shugaban Syria Bashar Al-Assad, yayin wata ziyara kasar Turkiya a ranar 8 ga watan Mayun 2010 ASSOCIATED PRESS - IBRAHIM USTA
Talla

Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad na wata ziyarar aiki a Hadaddiyar Daular Larabawa, wadda ita ce ziyararsa ta biyu a yankin tekun Gulf tun bayan girgizar kasar da aka yi a Syria a farkon watan Fabrairu, a daidai lokacin da kasashen Larabawa da dama ke sabunta hulda da Syria.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ruwaito cewa, Shugaba Assad na tare da mai dakinsa Asma, a ziyarar aiki ta farko da uwargindan sa ta kai kasar waje tun bayan barkewar rikici a kasar Syria a shekarar 2011.

Shugaba Assad tare da rakiyar Sarkin Oman
Shugaba Assad tare da rakiyar Sarkin Oman AP

Shugaba Assad dai ya kasance saniyar ware a fannin diflomasiyya tun shekara ta 2011 don murkushe boren jama'a wanda ya rikide zuwa yakin basasa. Tun bayan girgizar kasa a Syria, kasashen Larabawa sun kara kaimi tare da aikewa da kayan agaji zuwa Damascus.

A yayin taron Shugaba Assad ya yaba da rawar da wasu kasashen na Larabawa ke takawa wajen karfafa dangantakar dake tsakanin su  Larabawa, yana mai cewa kamata ya yi su zama 'yan uwan ​​juna, a cewar wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta Syria ta fitar.

Shugaban kasar Syria, wanda aka kori kasarsa daga kungiyar kasashen Larabawa a karshen shekarar 2011, ya ziyarci masarautar Oman a ranar 20 ga watan Fabrairu, wanda shi ne na farko cikin shekaru goma sha biyu na yakin Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.