Isa ga babban shafi

Israíla ta sha alwashin zafafa hare-hare kan Gaza gabanin shirin kutsawa ta kasa

Rundunar sojin Isra’ila ta ce za ta zafafa ruwan wutar da take yi a Zirin Gaza, wanda  ke  karkashin ikon kuniyar Hamas, gabanin shirin da ta ke na kutsawa yankin ta kasa, a yayin da hukumomin Majalaisar Dinkin Duniya ke gargadin kazancewar matsalar jinkai a yankin  na Falasdinawa. 

Hayakin da ya turnike sararin samaniya bayan harin Israíla a kan Zirin Gaza a ranar Jumaá, 20 ga watan Oktoba 2023.
Hayakin da ya turnike sararin samaniya bayan harin Israíla a kan Zirin Gaza a ranar Jumaá, 20 ga watan Oktoba 2023. AP - Francisco Seco
Talla

Kashin farko na kayan agaji sun isa wannan yankin da aka wa kawanya daga Masar a  jiya Asabar, amma an bayyana manyan motocin dakon kayan, makare da kayan agaji da aka bari su shiga wannan yankin a matsayin digo a cikin teku, duba da bukatun mazauna da suka kai miliyan 2  da dubu dari 3. 

Sojin Isra’ila ta yi ta luguden wuta a kan Zirin Gaza a matsayin martani ga harin da mayakan Hamas suka kai kasarta  ranar  7 ga watan Oktoba, wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutane dubu 1 da  dari 4. 

Hare-haren da Isra’ila ta ke kai wa a matsayin ramuwar gayya ta yi sanadin mutuwar Falasdinawa sama da dubu 4, kamar yadda kungiyar Hamas, wadda ke iko da Zirin Gaza ta sanar.

Wannan lamari ya janyo wa Isra’ila caccaka daga sassan  duniya, musamman ma kasashen Larabawa, amma Fira  Minista Benjamin Netanyahu ya zake cewa ana kai hare-haren ne a mabuyar mayakan kungiyar Hamas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.