Isa ga babban shafi
Najeriya

Hukumomin tsaro sun bada dalilan neman dage zabe a Edo da ke Najeriya

Hukumomin ‘yan sandan Najeriya da kuma leken asiri ta DSSm sun ce bukatarsu ta neman dage zaben gwamna a jihar Edo yana da nasaba da bayanan sirri da suka samu cewa ‘yan ta’adda na shirin kai hare-hare domin hana gudanar da zaben.

Neman dage zaben Edo ya haifar korafi
Neman dage zaben Edo ya haifar korafi Channels tv
Talla

A cewar hukumomin tsaron biyu, cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar, ‘yan ta’adda suna shirin kaddamar da jerin hare-hare yayin bukukuwan Sallah a ranakun 12 da 13 ga watan Satumba da muke ciki, kuma jihar Edo na daga cikin jihohin ake shirin kaiwa harin.

A cewar Don Awuna, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Najeriya dage zaben gwamnan zai bawa hukumomin tsaron kasar damar dakilewa tare da magance duk wata barazanar tsaro da ka iya tasowa yayin gudanar da zaben gwamnan dama lokacin bukukuwan Sallah.

Sai dai kuma a bangarenta babbar Jam’iyyar adawa a Najeriya ta PDP, reshen jihar ta Edo tayi zargin cewa hukumomin tsaron sun hada baki ne da jam’iyya mai mulki ta APC domin samun hanyar yin magudi a zaben kasancewar suna fargabar fuskantar shan kaye a zaben.

 

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.