Isa ga babban shafi
Lagos

Jihar Lagos na shirin kafa dokar kashe masu garkuwa da mutane

Gwamnatin jihar Lagos ta bi sahun wasu jihohin kasar da suka hada da Edo da Ogun da Anambra wajen sanya dokar kisa kan masu satan mutane suna garkuwa da su.

Gwamnan jihar Lagos Akinwumi Ambode
Gwamnan jihar Lagos Akinwumi Ambode
Talla

Wani dan majalisar Lagos Mudashiru Obasa ya gabatar da dokar dake cewa duk wanda aka samu da hannu wajen sace mutun ko garkuwa da mutun to kuwa hukuncin kisa ya rataya a wuyansa.

Tun a jiya Juma'a aka gabatarwa zauren majalisar Dokokin jihar ta Lagos wannan shirin kafa doka.

Karkashin dokar  duk mutumin da ya bari aka yi amfani da muhallin sa aka ajiye mutumin da aka sato ake garkuwa dashi to shima  gidan kaso na tsawon shekaru 14 ya kamashi babu tara.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.