Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram na fama da talauci- MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, kungiyar Boko Haram da aka karya lagwanta a Najeriya na fama talauci.

Mayakan Boko Haram
Mayakan Boko Haram AFP PHOTO / BOKO HARAM
Talla

Wani babban jami’in Majalisar Jeffery Feltman ya sanar da haka a yayin gabatar wa kwamitin tsaro da wani rahoto kan yadda Boko Haram ke barazana ga zaman lafiyar duniya.

Jami’in ya lura cewa, mayakan Boko Haram na fuskantar matsin lamba daga bangren sojoji, amma ya yi gargadi game da sakaci saboda yiwuwar kaddamar da sabbin hare-hare.

Mr. Feltman y  ce, kungiyar Boko Haram na ci gaba da zama babbar barazana lura da tarin mayakan da take da su.

Sai dai matsalar rashin kudi da kuma rarrabuwar kawuna da ya tilasta wa kungiyar darewa gida biyu, na cikin abubuwan da ke kara durkusar da ayyukan kungiyar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.