Hatsarin jirgin kasa ya kashe mutane a Legas
Rahotanni daga birnin Legas da ke kudancin Najriya na cewa, mutane da dama sun rasa rayukansu bayan wani jirgin kasa ya kauce hanyarsa a garin Agege a wannan safiya.
Wallafawa ranar:
Mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Olarinde Famous-Cole ya tabbatar da aukuwar lamarin, in da ya kara da cewa, jirgin ya kuma ci karo da wata katuwar motar daukan kaya.
Famous-cole ya ce, a yanzu haka, an tura jami’an tsaro wurin da hatsarin ya faru amma bai bada alkaluman mutanen da suka mutu ba.
Ba a karon farko kenan ba da ake samun hatsarin jirgin kasa a garin Agege mai cike da hada-hadar jama’a.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu