Isa ga babban shafi
Najeriya

Kwankwaso ya lashi takobin kayar da Buhari

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na jihar Kano ya kaddamar da aniyarsa ta tsayawa takara a zaben 2019 karkashin inuwar jam'iyyar PDP mai adawa a wani taron gangami da ya gudana a birnin Abuja, in da ya lashi takobin karbe kujerar mulki daga hannun shugaba Muhammadu Buhari.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ayyana aniyarsa ta tsayawa takaran shugabancin Najeriya a zaben 2019
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ayyana aniyarsa ta tsayawa takaran shugabancin Najeriya a zaben 2019 Premium Times
Talla

Taron Kwankwaso ya gudana ne a ranar Laraba a Otel din Chida de ke Utako a birnin Abuja bayan hana shi amfani da dandalin Eagle Square.

Taron ya samu halartar magoya bayan tsohon gwamnan na Kano daga sassa daban daban na Najeriya kuma yawancinsu sun sanya jajayen huluna don nuna goyon bayan ga Kwankwaso da aka san shi da sanya jar hula.

A dogon jawabin da ya gabatar, Kwankwaso ya yi alkawarin tunkarar matsalar tsaro da bunkasa tattalin arziki da inganta kayayyakin more rayuwa da bayar da ilimi matukar aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Sai dai baya ga Kwankwaso akwai tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da gwamnonin jihohin Sokoto da Gombe Aminu Tambuwal da Ibrahim Dankwambo da tsoffin gwamnoni  Jigawa da Sokoto, Sule Lamido da Attahiru Bafarawa da dukkaninsu ke neman tikitin tsayawa takaran shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP.

A bangare guda shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Bukola Saraki ya soki matakin hana Kwankwaso amfani da dandalin don kaddamar da aniyarsa ta tsayawa takaran shugabancin kasar a zaben 2019.

A wata sanarwa da mashawarcinsa na musamman kan harkokin yada labarai ya sanya wa hannu, Saraki ya ce, dandalin Eagle Sqaure mallakin daukacin al’ummar Najeriya ne.

A cewar Saraki, wannan matakin na nuna yadda kyama ta yi kamari a harkokin siyasar kasar da kuma demokradiya.

A ranar Talata ne hukumomin da ke kula da dandalin suka aika wasika ga Kwankwaso da ke sanar da shi matakin haramta masa amfani da dandalin duk da cewa da farko an ba shi izinin amfani da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.