Isa ga babban shafi
CIN ZARAFIN MATA

Kashi 48 na matan Najeriya na fuskantar cin zarafi - MDD

Yayin da yau ake bikin ranar yaki da cin zarafin mata ta duniya, Majalisar Dinkin Duniya tace akalla mata kashi 48 a Najeriya suka fuskanci nau’in cin zarafi daban daban tun bayan barkewar annobar korona a duniya.

Alamar yaki da cin zarafin mata
Alamar yaki da cin zarafin mata © Premium Times
Talla

Wani rahotan ofishin majalisar dake kula da mata yace kashi 23 na wadannan mata sun fuskanci matsalolin da suka hada da cin zarafin su da hana su hakkokin su, yayin da kashi 21 suka fuskanci matsalar sadarwa sakamakon takaita mu’amala domin dakile annobar, wadanda suka hada da killace jama’a a gida da dokar hana fita da kuma bada tazara.

Majalisar ta kuma ce kashi 16 na wadannan mata sun gabatar da korafi akan zargin cin zarafin su ta hanyar mu’amala, yayin da wasu kashi 15 suka gabatar da rahotan cin zarafin kai tsaye.

Mataimakin shugaban Najeriya  Yemi Osinbajo tare da wasu daga cikin 'yan matan Chibok 21 da Boko Haram ta saka
Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo tare da wasu daga cikin 'yan matan Chibok 21 da Boko Haram ta saka Sunday Aghaeze/Special Assistant to Nigerian President Muhammadu

Rahotan da yayi nazari akan kasashe da dama, yace kashi 45 daga cikin matan da aka gudanar da bincike akan su sun fuskanci wani nau’in cin zarafi na kai tsaye ko kuma na bayan fage.

Majalisar tace an gudanar da binciken ne a kasashen duniya 13 da suka hada da Albania da Bangladesh da Kamaru da Colombia da Cote d’Ivoire da Jordan da kuma Kyrgyztan.

Sauran sun hada da Morocco da Najeriya da Paraguay da Thailand da kuma Ukraine.

Buhari da uwargidan sa Aisha da wasu daga cikin matan shugabannin Afirka
Buhari da uwargidan sa Aisha da wasu daga cikin matan shugabannin Afirka © Nigeria presidency

Rahotan hukumar kula da jama’a a Najeriya yace kashi 30 na matan dake tsakanin shekaru 15 zuwa 49 suka fuskanci cin zarafin dake da nasaba da fyade a shekarar 2018, yayin da hukumar yaki da cin zarafin mata ta jihar Lagos tace mata 3,193 suka gabatar da korafin cin zarafin su tsakanin watan Janairu zuwa Disambar shekarar 2020.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.