Isa ga babban shafi
Nijar

Nijar ta bukaci ‘Yan kasa tallafawa ‘Yan wasan Mena

Kasar Jamhuriyyar Nijar ta bukaci tallafin kudi daga ‘yan kasar domin cika gibin kasafin kudin kasar CFA Biliyan 2 don tallafawa ‘Yan wasan Mena da ke shirye shiryen shiga gasar cin kofin Afrika.

Tutar kasar Jamhuriyyar Nijar
Tutar kasar Jamhuriyyar Nijar
Talla

A cewar kakakin kungiyar masoya ‘yan wasan Mena, suna neman tallafi da goyon bayan ‘yan Nijar domin ci samun nasara da cigaban ‘yan wasan Mena a gasar cin kofin Afrika da za’a gudanar a hadin gwiwar kasashen Gabon da Equatorial Guinea.

Hanyoyin da hukumar zata samu tallafin a cewar Djamila, sun hada da cire kudi CFA 10 ga wayoyin salula da ake kira a waje domin tallafawa ‘yan wasan Mena.

Wannan dai shi ne karo na farko da Jamhuriyyar Nijar ta samu shiga gasar cin kofin Africa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.