Isa ga babban shafi
Nijar

Jami'an tsaron Nijar sun dakile wani harin ta'addanci

Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun dakile wani harin ta’addanci da aka shirya kaddamarwa kan wani gidan yari mai cikakken tsaro a kusa da babban birnin Yamai kamar yadda Ministan Cikin Gidan kasar, Bazoum Mohamed ya sanar.

Gidan yarin Koutoukalé na Jamhuriyar Nijar
Gidan yarin Koutoukalé na Jamhuriyar Nijar RFI/Moussa Kaka
Talla

Majiyar tsaro ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa cewa, kimanin ‘yan ta’adda 10 ne dauke da makamai suka yi kokarin kai farmakin akan gidan yarin da misalin karfe biyar na yammacin jiya Litinin, amma an yi nasarar fatattakar su saboda jami’an tsaro na cikin shriin ko-ta-kwana.

Ministan Cikin Gidan Kasar, Bazoum Mohamed ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa, babu mutun ko guda da aka kashe a farmakin.

Gidan yarin na Koutoukale da maharan suka dosa, nada nisan kilominta 50 daga yammacin birnin Yamai, kuma akwai mayakan jihadi da dama da suka hada da mayakan Boko Haram da ake tsare da su a cikinsa.

Jami’an tsaro sun ce, maharan sun fara kutsawa cikin kasuwar Koutoukale,inda suka shirya yadda za su aiwatar da farmakin nasu da bai yi nasara ba.

A cikin watan Oktoban shekarar 2016, wasu mahara akan babura sun kai wa wannan gidan yarin farmaki,inda suka tayar da abubuwan fashewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.