Isa ga babban shafi

Faransa ta tabbatar da mutuwar 'yan kasar ta 6 a Nijar

Fadar Shugaban Faransa ta tabbatar da kashe wasu Yan kasar guda 6 dake yawon bude ido a Jamhuriyar Nijar tare da abokan rakiyar su Yan Nijar biyu lokacin da Yan bindiga akan Babura suka bude musu wuta.

Wasu sojojin jamhuriyar Nijar
Wasu sojojin jamhuriyar Nijar ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Fadar shugaban Faransa tace shugaba Emmanuel Macron ya tattauna da takwaran sa na Nijar Mahamadou Issofou ta waya kan lamarin.

Gwamnan Jihar Tilaberi yace Yan bindigar sun kashe mutane 8 ne cikin su harda Yan kasar Faransa 6 dake yawon bude ido.

Wata majiya ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar Yan bindigar dake kan Babura sun kai hari kan bakin ne da misalign karfe 11.30 na safiyar yau a wajen garin Koure dake da nisan tafiyar awa guda daga birnin Yammai.

Majiyar tace an harbi mutanen 8 ne da bindiga domin sun samu kwanson harsasai kusa da gawarwakin su, sai dai basu san wadanda suka aikata kisan ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.