Tawagar ECOWAS ta sake komawa Nijar don ganawa da sojoji da suka yi juyin mulki
Tawagar Kungiyar kasashen Afirka ta Yamma, wato ECOWAS ta isa birnin Yammai na Jamhuriyar Nijar domin ganawa da sojojin da suka yi juyin mulki a kasar. Tawagar wadda ke karkashin jagorancin tsohon shugaban mulkin soji na Najeriya, Janar Abdusalami Abubakar, na kuma dauke da mai alfarma Sarkin Musulmin kasar, Muhammad Sa’ad Abubakar tare da wasu jami’an ECOWAS.
Wallafawa ranar:
Firaministan da sojoji suka nada Ali Muhammad Lamine Zeine ne ya karbi tawagar a filin jirgin saman Yammai bayan isarta kasar, yayin da rahotanni ke bayyana cewar ana saran ta gana da shugaban sojin da ya jagoranci juyin mulki, Janar Abderahmane Tchiane da kuma shugaba Bazoum Mohammed.
Wannan ce ziyara ta biyu da wannan tawaga ta kai Nijar, bayan wadda ta kai a baya, wanda shugaban sojin yaki karbar su.
Wannan ziyarar kuma tana zuwa ne kwana guda bayan kammala taron hafsoshin sojin kasashen Afirka ta Yamma wanda ya gudana a kasar Ghana.
Hafsoshin sun ce sun kammala duk wani Shirin da ya dace domin mayar da mulkin farar hula a Nijar, abinda suke jira kawai shine umarni daga shugabannin kasashen wadanda ke ci gaba da daukar matakan diflomasiya domin ganin an kaucewa daukar matakin sojin.
A ziyarar da malaman addinin Islama daga Najeriya suka kai a makon jiya, a karkashin jagorancin Sheikh Bala Lau, sojojin sun bayyana musu aniyar tattaunawa da ECOWAS da kuma bukatar ganin an cirewa kasar takunkumin karya tattalin arzikin da aka kakabawa Nijar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu