Isa ga babban shafi

Mecece gaskiya kan batun janye dakarun Nijar daga Tafkin Chadi ?

Rahotanni na cewa, yaki da ta'addanci a yankin tafkin Chadi na iya fuskantar koma baya, sakamakon janye sojojin Jamhuriyar Nijar daga cikin rundunar hadin gwiwa ta kasashen yankin da ta kunshi Najeriya da Kamaru da Chadi da Nijar da kuma Benin.

Wasu sojojin jamhuriyar Nijar da ke taimakawa Najeriya wajen yaki da kungiyar Boko Haram.
Wasu sojojin jamhuriyar Nijar da ke taimakawa Najeriya wajen yaki da kungiyar Boko Haram. AFP - PHILIPPE DESMAZES
Talla

 

A shekarar 2014 aka kafa tawagar MNJTF, kuma ta fara aiki a shekarar 2015 da kimanin dakaru 10,000, domin tunkarar matsalar tsaro da mayakan Boko Haram suka haddasa a yankin tafkin Chadi.

Hedikwata a N'Djamena

Rundunar, mai hedikwata a N’Djamena na kasar Chadi, ta samu izini daga Tarayyar Afirka a watan Maris 2015.

Sojojin hadakar da ke karkashin rundunar hadin gwiwa ta MNJTF daga Najeriya da Nijar da kuma Kamaru sun samu nasarar kashe mayakan ISWAP fiye da 100.
Sojojin hadakar da ke karkashin rundunar hadin gwiwa ta MNJTF daga Najeriya da Nijar da kuma Kamaru sun samu nasarar kashe mayakan ISWAP fiye da 100. © MNJTF

Bayan juyin mulkin da sojoji suka yi na baya-bayan nan, an ce Nijar ta fice daga kungiyar, sakamakon takunkumai da ECOWAS ta kakabawa kasar da kuma da dakatar da ita daga kungiyar.

Wasu majiyoyi sun ce, wannan gibi da rashin Nijar din ya haifar na iya dagula al’amuran tare da karuwar hare-haren da ake kai wa a yankin tafkin Chadi tare da kwararar tarin makamai da mayakan kungiyar ISIS da ke arewacin Afirka zuwa yankin.

Tabbatar da tsaron cikin gida

Sai dai wasu bayanai daga Nijar na cewa, ba wai ta fice daga kungiyar ba ne, sai dai ta janye sojojinta ne domin kara tabbatar da tsaron kasar, saboda barazar kai mata hari da ECOWAS ta yi bayan juyin mulki.

Masanin Tsaro a Najeriya Dakta Yahuza Ahmad Getso ya yi mana karin bayani kan tasarin halin da ake ciki.

Muryar masanin tsaro Dr. Yahuza Ahmad Getso
01:01

NIGER 2023-11-21 GETSO

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.