Isa ga babban shafi

Shettima ya fice daga rumfar kada kuri'a sabo da rashin halartar jami'an INEC

Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Kashim Shettima, a  yau asabar ya isa mazabarsa ta Shettimari mai lamba 001 a unguwar Lawan Bukar da ke cikin birnin Maiduguri, amma ya kasa kada kuri’a saboda rashin halartar jami’an zabe.

Tsohon gwamnan jihar Borno kenan, lokacin da yake kada kuri'a a mazabarsa da ke jihar.
Tsohon gwamnan jihar Borno kenan, lokacin da yake kada kuri'a a mazabarsa da ke jihar. © premiumtimes
Talla

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Kashim Shettima ya isa rumfar zaben ne da misalin karfe 10 na safe inda ya gana da sauran masu kada kuri’a da dama suna jiran isowar kayan zabe da jami’an zabe.

Dan takara Shettima, wanda ya samu rakiyar gwamnan jihar, Babagana Zulum,Gwamnan jihar Borno,tawagar ta jira kusan mintuna 10 kafin ta fice.

A halin da ake ciki, an fara kada kuri'a a rumfunan zabe da dama a cikin babban birnin Maiduguri dake jihar ta Borno.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ta rahoto cewa hukumar zaben kasar INEC ta bayyana cewa masu kada kuri’a 87,209,007 daga cikin 93,469,008 da suka yi rajista sun karbi katin zabe na dindindin (PVCs) kuma ana sa ran za su kada kuri’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.