Isa ga babban shafi
Faransa

Hollande ya zargi Sarkozy da gurgunta tattalin arzikin Faransa

Dan Takaran shugaban kasar Faransa, a Jam’iyar Socialists, Francoise Hollande, ya zargi shugaba Nicolas Sarkozy da durkusar da tattalin arzikin kasar shekaru biyar da ya kwashe yana shugabancin kasar.  

François Hollande Dan takarar Jam'iyyar Socilalist a zaben shugaban kasar Faransa
François Hollande Dan takarar Jam'iyyar Socilalist a zaben shugaban kasar Faransa REUTERS/Regis Duvignau
Talla

Hollande ya bayyana Sarkozy a matsayin shugaban masu galihu, yace yanzu haka ya san cewar, cikin Sarkozy da magoya bayansa ya duri ruwa, domin babu lokacin da zasu iya kawo sauyi, don bunkasa rayuwar Faransawa.

Wannan kuma na zuwa ne bayan wani zaben jin ra’ayin jama’a da aka gudanar inda sakamakon zaben ya nuna Hollande zai lashe zaben da za’a gudanar a ranar 22 ga watan Afrilu, hakan ne kuma ya karfafa masa kwarin gwiwa.

Shugaba Sarkozy yana daga cikin shugabannin da suka taka rawa wajen ceto darajar kudin Euro da matsalar tattalin arzikin Turai wanda ya kara masa magoya baya duk da sukar da shugaban ke sha daga ‘yan adawa.

A sakonsa na sabuwar shekara shugaban ya sha alwashin fito da hanyoyin daidaita tattalin arzikin kasar Faransa tare da kiran ‘Yan kasar yin taka tsantsan a lokocin da zasu kada kuri’arsu a zaben shugaban kasa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.