Shugaban EU ya kare tsarin kafa Asusun gaggawa
Shugaban Kungiyar Kasashen Turai Herman Van Rompuy ya kare tsarin kasashen na kafa Asusun gaggawa na musamman domin tallafawa wasu kasashen Nahiyar da ke fama da matsalar tattalin arziki.Yunkurin kafa asusun tallafawa kasashen, ya biyo bayan rage karfi da darajar iya biyan bashin kasashen da aka yi.
Wallafawa ranar:
Herman Van Rompuy ya bayyana haka ne bayan ganawa da Fira ministan kasar Spain Mariano Rajoy a birnin Madrid, kuma yace Kamfanin Standards and Poor’s da ya rage mukamin Turai babu wani kokarin da yake yi domin daidaita dimbin basukan da ke wuyan wasu kasashen .
Yace a taron da zasu yi cikin watannin na wannan shekarar zasu duba dacewar yin kwaskwarima ga Hukumomin kudaden na Turai.
Yace Asusun na musamman zai kasance yana samun taimako daga kasashen da ke cikin kungiyar Turai masu amfani da kudaden Euro,
Shugaban yaceu Kungiyar kididdigan kudaden Fitch da Moody tana da kwarin gwiwa akan kasashen Turai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu