Isa ga babban shafi
Faransa-Turkiya

Faransa ta yi watsi da barazanar Turkiya akan dokar Armeniyawa

Gwamnatin kasar Faransa ta yi watsi da duk wata barazana da kasar Turkiya ke yi na kokarin mayar da martani game da amincewa da dokar hukunta duk wanda ya musanta kisan kiyashin Armeniyawa a zamanin mulkin Othman.

Nicolas Sarkozy Shugaban kasar Faransa.
Nicolas Sarkozy Shugaban kasar Faransa. Reuters/Robert Pratta
Talla

Nan da makwanni biyu ne shugaban Faransa Nicolas Sarkozy, zai rattaba hannu akan dokar bayan amincewar majalisar Dattawan kasar.

Wata majiya daga fadar Shugaban Faransa ta tabbatar da cewa, Sarkozy zai sanya hannu ba tare da wata tantama ba.

Bayan amincewa da dokar ne gwamnatin kasar Turkiya ta yi Tir da Allah waddai da Faransa.

A ranar Litinin ne Majalisar Dattawan Faransa ta amince da dokar hukunta duk wani mutum, wanda ya musanta kisan kiyashin da Turkiya ta yi wa Armenia a shekarar1915.

'Yan Majalisu 86 daga cikin 127 suka amince da dokar, wanda ta tanadi hukuncin daurin shekara guda ga duk wanda yace Turkiya bata aikata laifin ba, da kuma tarar kudi Euro 45,000.

Kasar Turkiya ta bayyana dokar a matsayin rashin hankali, yayin da take cewa, zata dauki kwararan matakai kan Faransa a nan gaba.

A baya dai gwamnatin Turkiya ta janye jekadanta daga kasar Faransa bayan da karamar Majalisar kasar ta amince da sabuwar dokar kafin mayar da shi domin daukar matakan hana majalisar Dattawa amincewa da dokar.

Ana dai zargin kasar Turkiya da kisan Armeniyawa 1915 a zamanin mulkin Othman wanda aka danganta da aikata laifukan yaki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.