EU-Birtaniya-Czech
Birtaniya da Czech sun ki amincewa da bukatar Turai
Kasashen Turai 25 daga cikin 27 sun amince da yarjejeniyar sa ido kan kasafin kudi, a taron shugabanin kasashen kungiyar, amma Birtaniya da Jamhuriyar Czech sun ki amincewa da shirin da ake kokararin samar domin kaucewa samun gibi.
Wallafawa ranar:
Talla
Fira Ministan Birtaniya, David Cameron, yace muddin matakin ya yi karo da muradun kasarsa, to zasu dauki mataki akai.
A cewarsa Birtaniya ba zata sanya hannunta ba akan yarjejeniyara, kuma zasu dauki mataki muddin suka fahimci shirin zai yi karo da manufofin Birtaniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu