Isa ga babban shafi
Faransa

Sarkozy zai bayyana shirin yin Tazarce a Faransa

A cikin wannan mako ne ake saran shugaban Kasar Faransa, Nicolas Sarkozy, zai kaddamar da shirin yin tazarce a zaben shugaban kasa, matakin da zai bude fagen fafatawa da Francois Hollande, Dan takarar Jam’iyyar Gurguzu ta Socialists.

Shugaban kasar Faransa, Nicolas Sarkozy wanda zai bayyana matakinsa na yin Tazarce a kan ragamar mulki
Shugaban kasar Faransa, Nicolas Sarkozy wanda zai bayyana matakinsa na yin Tazarce a kan ragamar mulki REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Yayin da ya rage makwanni 10 a gudanar da zaben shugaban kasar Faransa, yanzu haka kuri’ar jin ra’ayin jama’a na nuna cewar, shugaba Nicolas Sarkozy yana bayan Francois Hollande wajen farin jini masu kada kuri’a.

An dai zabe shi ne a ranar shida ga watan Mayu na shekarar 2007, inda ya kama aiki ranar 16 ga wata.

A lokacin shugabancinsa, Sarkozy ya kawo wasu sauye sauye da basu yi wa ‘Yan kasar dadi ba, da suka hada da baiw a jami’u cin gashin kansu da kare masu hali daga biyan harajin da ya dace da mayar da kasar kungiyar kawancen tsaro ta NATO, da kuma kara shekarun ritayar aiki daga shekarar 60 zuwa 62, abinda ya gamu da fushin yawancin ‘Yan kasar inda suka gudanar da yajin aiki da zanga-zanga.

Batun karbar kudaden yakin neman zabe daga attajira Lilian Betancourt ta hanyar da bata kamata ba, ya dada bata masa suna, abinda ya tilastawa Ministan kwadago, Eric Woerth sauka daga mukamin shi.

Rikici tsakanin shugaba Sarkozy da Tsohon Fira Ministan, Dominique de Villapine, ya kara wa shugaban abokan adawa.

Matsalar tattalin arzikin kasashen Turai na daga cikin abinda ‘Yan adawa ke sukar Sarkozy, inda kamfanonin sa ido ke rage darajar basukan kasar.

Amma Fira Minista Francois Fillon, yace wanan bai dame su ba, domin cikin makwanni uku zasu sauya ra’ayin jama’a game da zaben.

Ana saran Sarkozy zai fuskanci kalubale sosai daga Francois Hollande, sai dai Sarkozy yace, in dai har ya fadi zabe, babu wanda zai sake jin duriyarsa a cikin kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.