Isa ga babban shafi
Faransa

Sarkozy ya mayar da martani game da yankan Halal a Faransa

Shugaba Nicolas Sarkozy ya mayar da martani game da zargin da abokiyar karawar shi Marine Le Pen ta yi, cewa daukacin dabbobin da ake yankawa a kasar Faransa, ana yanka su ne ta hanyar Islama, tare da yin barazanar zuwa kotu.

Marine Le Pen 'Yar takarar neman kujerar shugaban kasar Faransa
Marine Le Pen 'Yar takarar neman kujerar shugaban kasar Faransa REUTERS/Pascal Rossignol
Talla

Sarkozy yace babu wata rufa rufa a cikin maganar, domin a cikin ton 200,000 na dabbobin da ake yankawa, kashi biyu da rabi ne kawai ake yankasu ta hanyar Islama.

Le Pen da ke hamayya da Sarkozy da Francois Hollande na Jam’iyyar Gurguzu tace zata shigar da kara game da al’amarin.

Sai dai Sarkozy a lokacin da ya ke yakin neman zabensa a birnin Rungis, Sarkozy ya soki Le Pen tare da cewa tana neman haifar da sa-in-sa ne tsakaninsu.

Naman da Al’ummar Musulmi ke ci shi ne wanda aka yanka bisa tsarin dokar Musulunci, kuma a tsarin Musulunci haramun ne a ci daman dabbar da ake kashewa ba tare da an yanka ba.

Sai dai wasu masu rajin kare hakkin dabbobi sun ce hakan keta hakkin dabba ne sabanin tsarin dokar da aka shata tsakanin kasashen Turai.

Sai dai Ministan cikin gidan Faransa Claude Gueant ya karyata zargin Le Pen inda yace akwai naman da ake yankawa a tsarin musulunci akwai kuma wadanda ake soke wa, kowannensu da alamar shi domin masu bukata.

A cewar Ministan, likitocin dabbobi sukan tabbatar da an sayarwa masu bukatar Naman halal ga masu bukata.

Le Pen dai tana bin hanyoyin da zata kamo kafafun Sarkozy da Hollande a yakin neman zabenta.

An dade dai Faransa na neman hanyoyin da zata amince da Musulmi a kasar, amma yanzu addinin Musulunci shi ne na biyu a kasar.

A ranar 22 ga watan Afrilu ne za’a gudanar da zaben shugaban kasa, a shiga zagaye na biyu a ranar 6 ga watan Mayu, sai dai zaben jin ra’ayin jama’a ya nuna Hollande akan gaban Sarkozy.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.