Dan bindigar Norway ya amsa rashin laifi bayan ya gurfana gaban Kotu
Anders Behring Breivik wanda ya amsa bindige mutane 77 a kasar Norway a watan Juli zai gurfana gaban kotu a Oslo inda wasu ke ganin yana da tabin hankali.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A ranar 22 ga watan Yuli ne, Breivik, ya kashe mutane Takwas bayan dala wani bom a wata mota da aka ajiye a harabar ginin ofishin Jens Stoltenberg, Fira ministan kwadago.
Daga nan ne kuma Breivik ya je Tsibirin Utoeya bayan ya yi shiga ‘Yan Sanda ya bude wuta a gungun matasa da suka halarci wani bukin Jam’iyyar Labour.
Wani binciken likitoci ya nuna, lafiyar Dan ta’addan kalau lokacin da ya kai harin, kuma shima da bakinsa ya amsa cewa da lafiyar shi.
Mista Breivik yace ya kai harin ne domin adawar shi da yadda Musulmi ke kutsa kai a Turai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu