Isa ga babban shafi
Faransa

‘Yan matan Hollande sun kunno ma shi baraka a Faransa

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya fara fuskantar barakar Siyasa bayan da budurwar shi Valérie Trierweiler, ta yada Sakon nasara ta Intanet ga abokin takarar tsohuwar budurwar shi da ta haifa ma shi 'Yaya Hudu Segolene Royal, a zaben ‘Yan majalisa

Valérie Trierweler  tare da Shugaban Faransa Francois Hollande .
Valérie Trierweler tare da Shugaban Faransa Francois Hollande . REUTERS/Bertrand Langlois/Pool
Talla

Sakon Valerie Trierweiler ya sa mutanen Faransawa suna ta cece-kuce, ganin yadda adawar da ke tsakanin matan biyu ya fito fili.

Royale, ita ce ta yi takarar zaben shugaban kasa, da Nicolas Sarkozy a shekarar 2007.

Kafofin yada labaran Faransa dai suna ganin wannan sakon na sabuwar buduwar shi abun kunya ne da kuma zai gurgunta farin jinin Jam’iyyar sabon shugaban.

Royar dai tana takarar kujerar Majalisa ne da Olivier Falorni a mazabar Yammacin birnin La Rochelle.

Bayan kammala zagayen farko na zaben ‘Yan Majalisu a ranar Lahadi, an yi hasashen Jam’iyyar Hollande da kawayenta zasu lashe yawan kujerun Majalisar.

Sai dai yanzu wannan barakar wani kwarin gwiwa ne ga Jam’iyyar UMP ta tsohon shugaba Nicolas Sarkozy wanda Hollande ya kada a zaben shugaban kasa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.