Farashin Kudin euro ya haura Dala a Asiya kafin taron shugabannin EU
Darajar kudin euro ta haura kudin Dalar Amurka a kasashen yankin Asiya, a dai dai lokacin da shugabannin kasashen Turai za su gudanar da taronsu a Brussels domin fito da hanyoyin magance matsalar bashin da ya addabi wasu kasashen masu amfani da kudin euro.
Wallafawa ranar:
Shugabannin kasashen dai suna cikin matsin lamba wajen ganin sun farfado da darajar euro a taron kwanaki biyu da za su gudanar a Brussels. Kodayake akwai matsalar bashi da ya dabaibaye wasu kasashen inda Cyprus da Spain suke neman tallafin gaggawa domin bin sahun Girka da Portugal da kuma Ireland.
Kasar Italiya ma tana fuskantar irin wannan barazana, duk da ita ce kasa ta uku cikin kasashe masu karfin tattalin arziki a Turai.
Yanzu haka kasashen Turai suna fuskantar matsin lamba daga kasashen Duniya wadanda suka bukaci shugabannin kasashen samar da wani tsari da zai inganta darajar kudin euro.
Kafin taron, shugabar gwamnatin Jamus Anglea Merkel da Shugaban kasar Faransa Francois Hollande sun yi wata ganawa ta musamman domin warwaren sabanin da ke tsakaninsu.
Yanzu tsawon shekaru uku ke nan kasashen Turai suna fama da matsalar tattalin arziki tare da kokarin fito da hanyoyin magance matsalar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu