Isa ga babban shafi
Faransa

Shugaba Hollande ya shiga rana ta biyu a ziyarar da ya ke yi a Maroko

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya shiga rana ta biyu a yau a ziyarar da ya ke gudanarwa a Maroko, inda a saukarsa birnin Casablanca a jiya, Hollande ya sami gagarumin tarbe daga sarki Mohammed IV.

Francois Hollade da Mohammed IV
Francois Hollade da Mohammed IV © AFP
Talla

Hollande, wanda ya bar karsar Faransa a daidai lokacin da kasar ta shiga wani hali na rikicin siyasa sakamakon abin kunyar kin biyan haraji da wani minista a gwamnatinsa ya yi, yana wannan ziyara ne domin karfafa alaka a fagage daban daban tsakanin kasarsa da kuma Maroko wadda daya ce daga cikin kasashen da ta yi wa mulkin mallaka.
Da farko dai ministoci da kuma manyan ‘yan kasuwar Faransa da ke tare da shugaba Hollande, sun sanya hannu a kan yarjeniyoyi akalla guda 12 da takwarorinsu na Maroko, yarjeniyoyin da suka ta’allaka a kan kasuwanci, ayyukan noma, sufuru, ilimi da kuma sabbin hanyoyin samar da makamashi na zamani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.