Isa ga babban shafi
France

Bincike ya gano kwayar cuta a cikin abincin jarirai a Faransa

Wata cibiyar binciken lafiya a Faransa tace akwai wata kwayar cuta da kwararru suka gano a cikin wani abincin da ake ba Jarirai a asibitin Alps inda ake tunanin cutar ce ta yi sanadiyar mutuwar jarirai a kwanakin baya. Wannan Binciken kuma na zuwa ne bayan iyaye sun shigar da kara domin kalubalantar wata asibiti a garin Chambery da ke kudu masu gabacin Faransa.

Ginin Cibiyar bincike lafiya a kasar Faransa
Ginin Cibiyar bincike lafiya a kasar Faransa Photo BSIP/UIG Via Getty Images
Talla

A watan Disemba ne aka samu mutuwar jaririai kusan guda uku a kwanaki jere da jere a wata asibiti da ke garin Chambery. Wannan ne kuma ya sa iyayen jariran suka shigar da kara domin kalubalantar asibitin.

Amma a wani bincike na kwararru daga wata cibiyar lafiya a Faransa tace akwai kwayoyin cuta da suka gano cikin abincin na gina jiki da ake ba jariran.

Kuma sakamakon binciken yace kwayoyin cutar suna da nasaba da muhalli da ba’a gano ba sai yanzu.

An dai gudanar da binciken ne ga jikkar abincin jariran kusan guda 10 amma a cewar Jean-Claude jami’in cibiyar binciken ba su gano musababin inda aka samo cutar ba ko hanyoyin da cutar da shafi abincin na jarirai.

Tuni gwamnatin Faransa ta bukaci a dawo da abincin na jarirai da aka rarraba a asibitoci guda bakwai a kasar bayan da aka gano abincin yana kisan jariran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.