Isa ga babban shafi
Faransa

‘Yan Majalisa sun amince da matakan tsuke aljihu a Faransa

Firaministan Faransa Manuel Valls ya samu rinjayen Majalisa ga kuri’ar amincewa da sabbin sauye sauyen tsarin tattalin arzikin kasar mai kunshe da matakan tsuke bakin aljihun gwamnati da ‘Yan Majalisa suka kada.

Manuel Valls,  Firaministan Faransa
Manuel Valls, Firaministan Faransa REUTERS/Charles Platiau
Talla

‘Yan Majalisar 265 ne suka amince da sabon tsarin yayin da 232 suka kada kuri’ar kin amincewa ga kasafin kudin mai kunshe da matakan tsuke aljihun gwamnati.

Wannan dai nasara ce ga sabuwar gwamnattin Firaminista Mannuel Valls duk da wasu ‘Yan Jam’iyyar Gurguzu na adawa da tsarin.

Sabon tsarin da ake gani naSshugaba Hollande da Valls yana kunshe ne da sabbin tsarin tsuke bakin aljihun gwamnati a wani mataki na kokarin farfado da tattalin arzikin Faransa.

Akwai kudi euro Biliyan 50 da aka datse a cikin tsarin da Majalisa ta amince, inda za’a rage kashe kudaden da ake kashewa nan da shekaru uku.

Tuni dai Valls ya bayyana farin cikinsa tare da yin na’am da amincewa da sabon tsarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.