Isa ga babban shafi
Girka

Jam’iyyar Syriza ta lashe zaben Girka

Shugaban Jam’iyyar adawa ta Syriza Alexis Tsipras zai karbi rantsuwar kama aiki a matsayin Firaministan kasar Girka, kamar yadda fadar shugaban kasa ta tabbatar. Tuni dai magoya bayan Jam’ iyyar Syriza da ke adawa da matakan tsuke bakin aljihu suka yi ta farin cikin nasarar zabe da suka samu a Lahadi inda suke fadin cewa nasarar da suka samu zai taimaka kasashen Turai su dawo daga rakiyar tsarin tsuke bakin aljihun.

Shugaban  Syriza, Alexis Tsipras
Shugaban Syriza, Alexis Tsipras REUTERS/Marko Djurica
Talla

Magoya bayan jam’iyyar sun yi ta bazama a birnin Athens suna daga tutocin jam’iyyar.

Jamiyyar Syriza na bukatar a sake tattauna yarjejeniyar kudi Euro biliyan 240 ne da kungiyar Tarayyar Turai da asusun bada lamuni na duniya suka bai wa Girka.

Firaministan Birtaniya David Cameron ya nuna matukar fargaba game da wannan nasara da jam’iyyar ta samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.