Isa ga babban shafi
Faransa

Iyayen da aka yi wa musanyar Jarirai za su karbi diyya

Wata kotu a kasar Faransa ta bayar da umarni ga wata Asibiti ta biya diyyar kudi euro miliyan biyu ga wasu iyaye guda biyu da aka yi wa musanyar jarirai a asibitin, shekaru sama da 20 da suka wuce.

Za a biya iyayen da aka yi wa musanyar jariri diyya a Faransa
Za a biya iyayen da aka yi wa musanyar jariri diyya a Faransa Reuters
Talla

Kotun ta bukaci Asibitin da ke birnin Cannes na Faransa ta biya iyayen diyyar kudi sama dad ala Miliyan 2 ga iyayen.

Wannan lamari dai ya auku ne a cikin shekarar ta 1994 lokacin da jariran biyu suka kamu da rashin lafiya inda aka saka su cikin kwalba guda don samar wa Jariran da magani, amma daga baya kuma sai wata ma’aikaciyar jinya ta musanya su wajen mika wa iyayen guda biyu jariransu.

Bayan shekaru 10 da aukuwar lamarin ne daga cikin iyayen Jaririn guda suka fahimci ‘yarsu ba ta kama da su kuma tana dauke da launin fata mai duhu, lamarin da ya sa suka shiga bincike don gano asalin ‘yarsu.

Binciken ne dai ya sa suka koma Asibiti don tabbatar da gaskiyar lamari, anan ne suka fuskanci cewa an yi mu su masanyen jariri.

Kotu yanzu ta umurci Asibitin ta biya kowanne jaririn da aka yi wa musanya kudin diyya euro dubu dari hudu, tare da biyan diyya ga iyayen jariran kudi euro dubu dari uku.

Daya daga cikin iyayen yaran mai suna Sophie Serrano mai shekaru 38 ta nuna farin cikinta da hukuncin, tana mai cewa bayan shafe tsahon lokaci yanzu an gano kuskure ne kuma kowa zai karbi ‘yarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.