Isa ga babban shafi
Girka-EU

Girka na neman cigaba da kasancewa cikin kungiyar EU

Gwamnatin Girka ta gabatar wa Kasashen Turai, Asusun Lamuni na duniya da kuma Bankin Tarayyar Turai da wasu sabbin shawarwari domin kaucewa dakatar da baiwa kasar basusuka kamar yadda wadannan cibiyoyi suka yi barazana.

Christine Lagarde Shugabar asusun bayar da Lamuni na IMF a zaman taro kan Girka
Christine Lagarde Shugabar asusun bayar da Lamuni na IMF a zaman taro kan Girka REUTERS/Francois Lenoir
Talla

Martin Salmayr, wani babban jami’i a ofishin shugaban Hukumar kungiyar tarayyar Turai Jean-Claude Juncker, shi ne ya tabbatar da cewa Girka ta gabatar da wadannan shawarwari a yammacin jiya Lahadi, a daidai lokacin da ministocin kudin kasashen ke shirin zaunawa a yau litinin domin daukar matakin karshe kan kasar.
A jiya lahadi, dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a biranen Brussels da Amsterdam don nuna adawa da yadda wadannan cibiyoyi da kasashe ke neman tursasawa Girka a game da wannan bashi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.