Isa ga babban shafi
EU

Kasashen Turai sun rattaba hannu kan yaki da safarar bakin haure

kasashen Turai sun rattaba hannu a wani kudurin doka tare da kafa runduna ta musaman domin yaki da masu safarar bakin haure a Birnin Luxembourg yayin da taron ya samu halartar ministocin kasashen yankin.

Taron bakin haure
Taron bakin haure REUTERS/Ismail Zitouny
Talla

Rundunar mai suna Eu Navfor Med kuma bisa jagoranci Amiral Enrico Credendino na kasar Italiya zata mayar da hankali wajen yaki da masu safarar bakin haure zuwa nahiyar turai.

Rudunar dai tana kunshe da sojojin ruwa na kasashen da suka bada goyan baya a wannan yunkuri na hana bakin haure kwarara yankin Turai.

A bangare guda, rundunar za ta mayar da hankali wajen lalata jiragen ruwan da ake amfani da su a safarar bakin haure, lamarin da ake sa ran zai kawo raguwar mace macen bakin hauren.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.