Isa ga babban shafi
Girka

Kasashen Turai sun kammala tattaunawa kan Kasar Girka

Ministocin kudi na kasashen Turai sun kammala tattaunawa kan batun Girka amma ba tare da sun cim ma matsaya ba, wannan kuma na zuwa ne kafin soma taron gaggawa na shugabannin kasashen kan rikicin dimbin bashin da ke kan wuyan Girka.

Taron Kasashen Turai masu amfani da Kudin euro
Taron Kasashen Turai masu amfani da Kudin euro REUTERS/Emmanuel Dunand/Pool
Talla

Kafin soma taron shugabannin kasashen Turai kan batun rikicin bashin Girka, ministocin kudi na kasashen sun kammala tattaunawa a Brussels ba tare da sun samu jituwa ba kan yadda za a shawo kan matsalolin kasar Girka da ke barazanar ficewa daga cikin kasashen da ke amfani da takardar kudin euro.

Akwai dai sabbin tsare tsare da Girka ta gabatar domin janyo hankalin masu binta bashi.

Sabbin tsare tsaren kuma sun hada da karin kudaden haraji da rage yawan shekarun Ritaya na Ma’ aikata, wanda wannan dama ce ga Girka ta cike gibin kasafin kudinta.

Masana dai na ganin sabbin tsare tsaren, mataki ne da zai iya kaiwa ga cim ma jituwa tsakanin Girka da masu binta bashi da suka hada da kungiyar Tarayyar Turai da babban bankin nahiyar da kuma asusun lamuni na duniya.

Akwai dai barazana ga Girka idan har masu binta bashi ba su gamsu da sabbin matakan da ta gabatar ba, kafin taron na shugabannin kasashen Turai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.