EU ta amince da sake matsuguni ga bakin haure
Shugabannin Kungiyar kasashen Turai sun amince su sake matsuguni ga dubban baki 'yan ci rani da suka isa kasahsen Italiya da Girka a wani taro da suka yi daren jiya.
Wallafawa ranar:
Shugaban taron Donald Tusk ya ce, za’a rarraba bakin haure dubu 40 zuwa wasu kasashen dake kungiyar a cikin shekaru biyu masu zuwa amma ba tare da sanya sharadi kan adadin da kowacce kasa za ta karba ba.
Sabbin alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewa bakin haure dubu 63 ne suka isa Girka ta ruwa a cikin wanna shekarar yayin da dubu 62 suka isa Italiya banda dubban da suka mutu.
Akasarin bakin hauren sun baro kasashensu ne saboda tashe tashwn hankula da kuma matsalar talauci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu