Isa ga babban shafi
Girka

An rufe Bankuna a Girka

Gwamnatin Kasar Girka ta bayar da umurnin rufe daukacin bankunan kasar har na tsawon mako guda inda ta bukaci hadin kan al’ummar kasar wadanda ke rige-rigen kwashe kudadensu a ATM.

Al’ummar Girka na jerin gwano wajen wawushe kudaden da ke cikin ATM.
Al’ummar Girka na jerin gwano wajen wawushe kudaden da ke cikin ATM. (©Reuters)
Talla

Girka ta kuma takaita adadin kudaden da ‘yan kasar za su iya cira a ATM zuwa yuro 60.

Girka tace bankunan kasar za su ci gaba da zama a rufe ne daga yau litinin zuwa ranar 6 ga watan gobe, kwana guda bayan kammala kuri’ar jin ra’ayin al’umma kan bashin kasar, sai dai hukumomin sun ce dokar ba za ta shafi baki ‘yan kasashen waje da yanzu haka suke cikin kasar ba.

Kungiyar Kasashen Turai ta bukaci matafiya da ke shirin zuwa Girka su yi tanadin kudi a aljihunsu kada su dogara da bankunan kasar.

Tun a karshen mako ne Al’ummar Girka ke jerin gwano wajen wawushe kudaden da ke cikin ATM.

Kungiyar Ma’aikatan Banki a Girka ta ce kimanin kudi yuro Biliyan da dubu dari uku mutanen kasar suka cira a ATM tun a ranar Juma’a. kuma zuwa Lahadi kungiyar tace an wawushe kudaden ATM kusan kashi 60.

Wannan matakin ya biyo bayan kin amincewa da bukatar Girka da kungiyar kasashen Turai ta yi na kara ma ta lokacin biyan bashin da ake bin ta bayan an kwashe kwanaki ana tattaunawa tsakanin wakilan kasar da na kungiyar Turai da kuma hukumar bada lamuni ta duniya.

Sakamakon daukar wannan matakin ya sa hannayen jari a Tokyo da Sydney sun fadi da kashi 2 a yau Litinin, yayin da darajar kudin yuro ta fadi.

Bankin kasashen Turai ya ce zai bar kofa bude dan kai wa kasar taimakon gaggawa idan hakan ya zama wajibi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.