Isa ga babban shafi
Girka-EU-IMF

Girka na tsaka mai wuya

Mahukuntan Girka sun koma teburin tattauna da hukumomin da ke bin kasar bashi domin samun mafita ga sabanin da ke tsakaninsu kan rikicin dimbin basukan da ke kan wuyan Girka.

Girka na iya ficewa Kungiyar  Turai da ke amfani da kudin yuro
Girka na iya ficewa Kungiyar Turai da ke amfani da kudin yuro Reuters/François Lenoir
Talla

Wannan na zuwa ne bayan Firaministan Girka Alexis Tsipras ya yi watsi tsarin da ma su bin kasarsa bashi suka gabatar a wajen tattaunawar da suke yi a Brussels abin da ya hana cimma yarjejeniya a jiya Laraba.

Daga cikin abin da wakilan Girka suka ki amincewa sun hada da zabtare kudin fansho da kuma kara haraji ga kamfanoni.

Girka na tattaunawa ne da Hukumar Turai da Babban Bankin Nahiyar da kuma asusun lamuni IMF wadanda ke bin kasar bashi.

Hukumomin na bukatar Girka ta biya kudaden da ake bin ta sama da dala Biliyan guda rabi kafin zuwa Talata, kafin kasar ta samu wasu kudaden tallafi.

Girka na iya ficewa daga kungiyar kasashen Turai masu amfani da kudin yuro idan har ba ta cim ma wa’adin ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.