Isa ga babban shafi
Girka

Shugabannin Turai sun gargadi Girka

Shugabannin Turai sun yi gargadi ga Girka akan ta gaggauta daukar matakan da suka dace don gujewa ficewa daga kungiyar kasashen da ke amfani da takardar kudin euro. Wannan na zuwa ne a yayin da mutanen Girka suka kaddamar da zanga-zangar adawa da sabbin matakan tsuke bakin aljihu da aka tursasawa kasar don samun wasu kudaden tallafi.

Firaministan Girka Alexis Tsipras ya gana da Shugaban Hukumar Turai Jean-Claude Juncker a Brussels
Firaministan Girka Alexis Tsipras ya gana da Shugaban Hukumar Turai Jean-Claude Juncker a Brussels REUTERS/Francois Lenoir
Talla

Manyan Shugabannin na Turai sun ja kunnen Firaminista Alexis Tsipras akan ya gujewa duk wasu matakan da za su sa Girka ta fice daga kungiyar kasashe masu amfani da kudin euro.

Shugabannin na Turai sun bukaci mahukuntan Girka su gaggauta amince wa da sabuwar yarjejeniyar bashi don samun wasu karin tallafin kudi.

A yau talata ne Shugaban hukumar Turai Jean-Claude Juncker, tare da wasu manyan Jami’an kungiyar Turai suka yi ganawa ta keke da keke tsakaninsu da Firaminsitan Girka bayan ya gana da shugabannin Jamus da Faransa.

Yanzu haka kuma sabuwar zanga-zanga ta barke a birnin Athens inda dubban mutane suka fito domin nuna adawa da sabbin matakan tsuke bakin aljihu da hukumomin da ke bin Girka bashi suka tursasa wa kasar.

A karshen watan nan ne dai wa’adin yarjejeniyar bashin Girka zai kawo karshe bayan an shafe shekaru 5 kasar na fama da dimbim bashi a wuyanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.