An cafke tsohon kwamandan Yugoslavia
Hukumomin kasar Montenegro sun kama wani tsohon janar din sojan kasar Yugoslavia, da ake zargi da aikata laifuka yaki a cikin shekarun 1990.
Wallafawa ranar:
Wata majiya daga Podgorica, babban birnin kasar ta Monténégro tace an kama Borislav Djukic, mai shekaru 66 a duniya, dan kabilar Serbia lokacin da ya ke kokarin shiga jirgin sama zuwa birnin Belgrade.
Tuni aka gurfanar da Djukica gaban wata kotun birnin na Podgorica, wadda ta bayar da umarnin ci gaba da tsare shi, har zuwa lokacin da za a mika shi zuwa kasar Croatia.
Ana zargin Janar din na Soja ne da aikata laifukan yaki tsakanin 1991 zuwa 1993 a yakin neman ‘yancin Croatia.
An kammala yakin ne a 1995 inda aka kashe mutane kimanin 20,000.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu