Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta dakatar da aikin neman Jirgin Malaysia

Faransa ta dakatar da aikin neman jirgin saman Malaysia da yayi hadari a tsibirin La Reunion dake tekun India bayan kwashe kwanaki 10 ana bincike ta jiragen ruwa da sama ba tare da cin nasara ba.

Masu aikin neman Jirgin Malaysia a tsibirin La Reunion na tekun India
Masu aikin neman Jirgin Malaysia a tsibirin La Reunion na tekun India REUTERS/Patrick Becot
Talla

Sai dai hukumomin tsibirin sun ce jami’an su zasu cigaba da sa ido ko Allah zai sa su ci nasara.

A ranar 29 ne ga watan jiya aka samu wani sashe na fiffiken jirgin kuma Firai ministan Malaysia ya tabbatar cewa sashen na jirgin ne wanda ya kwaso sama da mutane 200 daga birnin Kuala Lampur inda ya nufi birnin Beijing na Kasar China.

Gano sashen jirgin dai, ya bada kwarin gwiwar cewa hukumomin zasu samu damar bayar da cikakken bayani kan yadda jirgin ya yi hadari bayan ya yi batan dabo a ranar 8 ga watan Maris shekara ta 2014.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.