Isa ga babban shafi
Faransa-Jamus

Hollande da Merkel za su gana kan ‘yan ci-rani

Shugabannin kasashen Faransa da Jamus za su gana a yau Litinin a birnin Berlin domin tattauna matsalar ‘yan ci-rani da ke ci gaba da kwarara a kasashen Turai.Wannan na zuwa ne a yayin da Dubban ‘yan ci-rani da ‘yan gudun hijira yawancinsu mutanen Syria ke kutsawa ta Macedonia da Serbia domin shiga kasashen yammacin Turai.

REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Francois Hollande na Faransa za su tattauna matakan da za su dauka domin magance matsalar ‘yan ci rani da ke ci gaba da kwarara kasashen Turai.

Tarayyar turai ta bayyana matsalar ‘yan ci rani a matsayi mafi girma tun yakin duniya na biyu.

A ranar Assabar mahukutan Italiya sun ce jami’an ruwan kasar sun yi nasarar ceto bakin haure kusan 4,500 a cikin kwale kwale 22 da suke ci a tekun mediterannean. Adadi mafi girma da aka ceto a rana guda.

Tunisia ma ta ceto kwale-kwalen bakin haure 124 da ke son shiga Italia daga Libya, yawancinsu ‘Yan Afrika.

Yanzu haka kuma dubban bakin haure ne ke kokarin shiga macedonia da Serbia domin tsallakawa zuwa yammacin Turai.

Kuma akwai mata masu ciki da yara kanana da suka tagayyara a Macedonia bayan jami’an ‘yan sanda sun hana su tsallaka kan iyakar kasar da Girka.

Adadin dai bakin haure kimanin 107,500 suka tsallaka Turai a bana, kuma adadin na iya karuwa ganin yadda mutane ke ci gaba da kokarin shiga kasashen a kullum.
 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.