An tsinci mota shake da gawarwakin ‘Yan ci-rani 70 a Austria
Kimanin ‘Yan ci-rani 70 ne aka tsinci gawarwakinsu cikin wata budaddiyar mota saman hanya a kasar Austria kusa da kan iyaka da Hungary a jiya Alhamis, al’amarin da ya girgiza shugabannin Turai da ke tattauna hanyoyin da za su magance matsalar kwararar ‘Yan ci-rani.
Wallafawa ranar:
Ministan cikin gidan Austria Alexander Marakovits ne ya tabbatarwa Kamfanin dillacin labaran Faransa AFP da yawan adadin ‘Yan ci-ranin da aka tsinci gawarwakinsu a saman babbar hanya kusa da kan iyaka tsakanin Slovakia da Hungary.
Sai dai babu wani cikakken bayani akan ‘Yan ci-ranin game da asalinsu amma ‘Yan sanda a Austria na ci gaba da bincike akai.
An tsinci motar ne dai saman hanya babu kowa a ciki sai gawarwaki.
Wannan kuma na zuwa ne a yayin da kwale kwalen ‘yan ci-rani 30 suka nutse a tekun Mediterranean a daidai lokacin da shugabannin Turai ke tattauna matakan da za su dauka akan kwararar ‘yan ci-ranin da ke bi ta kasashen Balkans zuwa Nahiyar Turai.
Dubban ‘Yan ci-rani ne ke ci gaba da shiga Turai ta tekun Mediterranean, yawancinsu daga kasashen gabas ta tsakiya da Afrika.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu