Isa ga babban shafi
Faransa-Turai

EU zata tallafawa Faransa kan matsalar 'yan cirani

Hukumar Tarayyar Turai tace za ta baiwa Kasar Faransa tallafin Euro miliyan biyar, domin taimakawa dubban ‘Yan cirani da ‘Yan gudun hijara dake cikin mawuyacin hali a yankin Calais, yayin da matsalar kwararar bakin ke ci gaba da addabar nahiyar Turai.

Fraiministan Faransa Manuel Valls
Fraiministan Faransa Manuel Valls REUTERS/Jacky Naegelen
Talla

Mataimakin shugababa hukumar Kungiyar Turai ne, Frans Timmermans ya sanar da haka a ziyara da ya kai arewacin Faransa a yau Litinin, yayin da Fraiministan Faransa Manuel Valls ya bayyana cewa kasashen Turai kalilan ne ke kokarin shawo kan matsalar kwararar bakin, inda kuma akasarinsu ke kin daukan nauyin daya rataya a wuyansu, na baiwa bakin mafaka , lamarin da ya ce ya sabawa akidar Turai kuma ba za su amince da haka ba.

A bangare guda, jami’an ‘Yan Sandan Kasar Girka sun jefa wa dubban ‘Yan ci rani dake zanga zanga a kan iyakar Girka da Mercedonia hayaki mai sa hawaye, kuma zanga zangar na zuwa sakamakon matakin da Mercedonia ta dauka na rufe kan iyakarta na yan sa’oi, domin dakile kwararar bakin wadanda kuma ke yunkurin kutsawa kasar hungary.

Itama dai Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi kira ga sauran mambobin kasashen Turai, da su karbi wani kaso na bakin dake neman mafaka.

A ranar 7 ga watan gobe ne ministocin cikin gidan kasashen Turai zasu gana a birnin Brussels na kasar Belgium, domin tattauna yadda za’ a tunkari matsalar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.